TAKIYYA AWAJEN `YAN SHI`A

Jerin Littafan Shi’a Na 3


Akidar

Takiyya

a wajen

‘Yan Shi’a

 

 

Dr. Umar Labdo

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Ma’anar Takiyya ita ce bayyana savanin abinda yake zuci, watau mutum ya fadi sabanin abinda ya kudure a zuciyarsa, ko ya aikata wani aiki tare da nuna cewa ya yarda da aikin amma a zuciyarsa yana ganin aikin ba dai-dai ba ne, ko bai dace ba, ko kuma haramun ne.   Zai yi haka da niyyar jawo hankalin wasu, ko yaudarar su, da nuna musu kansa ba a hakikanin yadda yake ba.

Ayatullahi Khumaini ya bayyana ma’anar taqiyya a wajen ‘yan Shi’a, kamar haka: “Takiyya ma’anarta ita ce mutum ya fadi magana wacce ta savawa ainihin abinda yake akwai, ko ya aikata wani aiki wanda yake saba wa mizanin Shari’a.”[1]

Manufar Takiyya ita ce jawo hankalin mutane da samun yardarsu da soyayyarsu ta hanyar boye abinda aka san ba sa so, ko ba zai karbu ba a wajensu. Khumaini yana fadi dangane da haka, “An shar’anta Takiyya domin yin kara ga mutane da jawo soyayyarsu da kaunarsu.”[2] A wani wurin kuma ya ce, “Abin nufi da kara shi ne ya zama manufar ita ce hada kai da dayantaka ta hanyar jawo soyayyar masu sava mana da samun kaunarsu.”[3] Masu saba mana, a maganar tasa, su ne duk wadada ba ‘yan Shi’a ba.

‘Yan Shi’a sun san akidunsu ba za su tava karbuwa ba ga Musulmi, saboda sabawarsu ga Alkur’ani da Sunnah da hankali lafiyayye. Don haka suke boye su, su dauki salon yaudara da munafurci, wanda suke kira kara, don yada su da tallata su a tsakanin jama’a. Haka nan, suna daukar son iyalin gidan Annabi(SAW), Ahalul Baiti, a watsayin wani mayafi da suke lullube wannan munafurci nasu da shi.

Takiyya tana da muhimmanci sosai, da matsayi mai girma, da falala mai yawa a cikin tafarkin Shi’anci. Dangane da wannan, babban malaminsu, Muhammad binu Ya’akub Alkulaini, ya ruwaito daga Imaminsu na biyar Abu Ja’afar, wai ya ce: “Taqiyya tana daga addinina da addinin iyayena.   Kuma babu imani ga wanda bai da taqiyya.”[4]

Babu shakka dangana wannan riwaya ga Abu Ja’afar, Allah ya yi masa rahama, karya ce tsagwaronta; saboda Abu Ja’afar da iyayensa ba su san munafurci ko yaudara ba.

‘Yan Shi’a suna amfani da Takiyya a matsayin wani mayafi da suke lullube bidi’arsu da miyagun akidojinsu da shi. Suna da hanyoyi masu yawa na yin haka. Da farko dai, idan bai zama dole ba, dan Shi’a ya kan so ya boye hakikanin cewa shi dan Shi’a ne, musamman inda ya san mutane suna da wayewa game da kungiyar. Idan kuma asirinsa ya tonu, aka san cewa shi dan Shi’a ne, to sai ya yi kokarin nuna cewa ba wani abu ne Shi’a ba face kaunar iyalin gidan Annabi(SAW), watau Ahalul Baiti, da goyon bayan su da jibintar su.

Koda yake ‘yan Shi’a suna kudure matukar gaba da kiyayya ga Sahabban Annabi, wadanda suke daukar su a matsayin kafirai da suka yi ridda, amma suna boye wannan qiyayya da kuduri nasu, ba sa bayyana su ga mutane. Sau da yawa ma su kan yi musun hakan, kuma su kan nuna cewa kin Sahabbai wani mummnan abu ne wanda bai kamata a zarge su da shi ba. Amma littafansu da maganganunsu suna tabbatar da haka.

Haka nan, ‘yan Shi’a suna yin taqiyya dangane da Alkur’ani mai girma, inda suke nuna cewa su ma suna ban gaskiya da shi kamar sauran Musulmi, duk da yake suna kudure cewa wai Sahabbai sun yi sauye-sauye a cikinsa. Ga akidar Shi’a, Alkur’ani an yi kari da ragi a cikinsa, saboda haka ba dukkaninsa suka yarda da shi ba. Amma suna boye wannan kuduri nasu, su nuna cewa sun yarda da Alkur’ani dukkaninsa.

Wani salon Takiyya kuma da ‘yan Shi’a suke nunawa shi ne makirci a cikin alakar su da mutane. Za ka ga dan Shi’a yana yin kirki, yana haba-haba da mutane, kuma yana taimakon su, amma duk yana yin haka ne domin jawo hankalinsu da shigar da su tafarkin Shi’anci. A wani yayi, su kan gabatar da taimako da agaji ga marasa lafiya, ko mabukata, da sunan taimakon ‘yan uwa Musulmi, amma duka Takiyya ce. Manufarsu a koda yaushe ita ce jawo hankalin mutane wadanda ba su san hakikanin tafarkinsu ba.

Fagagen Takiyya

Takiyya a wajen ‘yan Shi’a tana shiga dukkanin fagage na addini da rayuwa. Suna yin Takiyya a cikin ma’amala, kamar yadda muka gabatar, kuma suna yin ta a cikin ibadoji da harkoki na yau-da-kullum.

Takiyya a Cikin Sallah

‘Yan Shi’a suna yin Takiyya a cikin sallah, kuma wannan yana ba su dama su yi sallah tare da Ahalus Sunnah domin su yaudare su. Koda yake suna daukar Ahalus Sunnah a matsayin kafirai, saboda ba su yi imani da Imamai ba kuma ba su barranta daga Sahabbai ba, amma yana halatta a gare su su bi su sallah, kuma sallar ta inganta ba sai sun rama ta ba, matukar dai da niyyar Takiyya suka yi ta.

Babban malaminsu, Ayatullahi Ruhullahi Khumaini, yana fadi dangane da kama hannu a sallah kamar haka: “Dora dayan hannaye a bisa dayan, kamar yadda masu saba mana suke yi, yana bata sallah idan an yi hakan da gan-gan. Amma babu laifi idan aka yi shi a bisa ga Takiyya.”[5] Masu saba mana, yana nufin Ahalus Sunnah.[6]

Magajin Khumaini, watau jagoran kasar Iran a yau, Ayatullahi Ali Khamna’i, da aka tambaye shi, ya ce: “Sallah na inganta a bayansu (Ahalus Sunnah) idan ya zama an yi ta saboda kara gare su.”[7] Kara, a maganarsa, tana nufin yaudara.

Har yau, an tambayi wani babban malamin nasu mai suna Ayatullahil Uzma Abul Kasim Alkhu’i: Shin sallah na inganta a bayan limami Ahalus Sunna? Sai ya ce, “Tana inganta idan an yi ta bisa Takiyya.”[8]

Shi kuwa Ayatullahi Muhammad Rida Musawi Kalbayakani cewa ya yi, “Babu laifi a yi sallah a bayansu tare da larura, amma idan ba larura to za’a rama sallar idan an samu ikon yin haka.”[9]

Mai karatu zai lura cewa sharadin sallar dan Shi’a a bayan Ahalus Sunna shi ne Takiyya ko larura. Idan larura ta sa shi, to zai rama idan ya samu iko. Amma idan ya yi bisa Takiyya ne to sallar ta inganta, kuma ba sai ya rama ba. A wani kaulin ma cewa aka yi zai samu lada, kamar yadda ya zo a wata ruwayar daga malaminsu, Kalbayakani, ya ce: “Sallah na inganta a bayan Ahalus Sunna a yayin Takiyya, kuma ladan hakan yana da yawa.”[10]

 

Takiyya a cikin Azumi da Hajji

Kamar yadda ya halasta ga dan Shi’a ya yi Taqiyya a sallah, haka nan ya halasta gare shi ya yi Takiyya a cikin azumi da hajji domin yaudarar Ahalus Sunnah.

Babban malamin Shi’a na wannan zamani, wanda ‘yan Shi’ar Nijeriya suke yin koyi da shi, Ayatullahi Khumaini, yana cewa: “A sani abinda ake fa’idanta daga ruwayoyi shi ne ingancin aikin da aka gina a kan Takiyya, sawa’un an yi Takiyyar ne saboda sabanin dake tsakaninmu da su (Ahalus Sunna) a hukunci, kamar shafa a kan huffi da buda baki da zarar gudan rana ya fadi, ko kuwa saboda savanin tabbatar faruwar wani abu, kamar kamawar wata, misali tsayuwar Arafa a ranar takwas ga wata saboda su a wajensu tara ne.”[11]

Abinda Khumaini yake fadi a nan shi ne, ruwayoyi daga Imaman Shi’a suna tabbatar da cewa duk aikin da aka gina shi a kan Takiyya ya inganta. Sai ya ba da misali da cewa, idan dan Shi’a ya yi shafa a kan huffi don ya yaudari Ahalus Sunna, ko ya gaggauta buda baki, to aikinsa ya inganta duk da cewa su a wajensu wadan nan abubuwa biyu ba sa inganta.

Kamar yadda aka sani, ‘yan Shi’a ba sa shafa a kan huffi (wanda Sunna ce ta Annabi (SAW) amma su ba su yarda da ita ba) kamar yadda ba sa gaggauta buda baki (wanda shi ma Sunna ce da suke musun ta) sai dai su jinkirta sai taurari sun fito.[12] Haka nan, idan dan Shi’a bai ga wata ba yana iya kama azumi tare da Ahalus Sunna a kan Takiyya kuma azumin nasa ya yi, kamar yadda yake iya tsayuwar Arafa ranar takwas ga watan Zul Hijja (a lissafinsa) idan Ahalus Sunna suka ce tara ne, kuma hajjinsa ya yi.

Duba ka gani, ya dan uwa mai karatu, wannan abin mamaki na ‘yan Shi’a. Su ba abinda ya dame su! Ko ina ta fadi sha ne a wajensu. Su dai su voye gaskiyar lamarinsu; kada a gane su. Wannan addini na ‘yan Shi’a da arha yake! Anya Allah ake nufi da wannan addinin?!

Takiyya a Jana’iza da Sallar Gawa

‘Yan Shi’a suna yaudarar Ahalus Sunna wajen halartar jana’izar mamatansu da yi musu sallah, amma ba addu’a suke yi musu ba; la’anar su suke yi. Wannan shi ne abinda manyan malamansu, kai har ma da Imamansu (a fadinsu) suke koya musu.

Wani malami daga cikin magabatansu mai suna Muhammad binu Muhammad binu Nu’uman wanda suke wa lakabi da Almufid, yana cewa: “Ba ya halasta ga wani daga cikin masu imani ya wanki mai saba wa gaskiya dangane da wilaya. Kuma kada ya yi masa sallah sai dai idan larura ta tilasta masa yin haka bisa ga Takiyya. To sai ya wanke shi irin wankin masu saba mana, kuma kada ya ba shi wasika.[13] Sa’an nan idan ya yi masa sallah, to sai ya la’ance shi, kada ya yi masa addu’a a cikinta.”[14]

Malaman Shi’a sun karbo ruwaya daga Imaminsu na shida, Abu Abdillah Ja’afar Sadiq (Allah ya rahamshe shi kuma ya isar masa karerayin da aka laqa masa) cewa wai, “Wata rana Hussaini binu Ali (Imami na uku ke nan a wajen ‘yan Shi’a, Allah ya kara masa yarda) ya fita zuwa jana’izar wani munafuki da ya mutu, sai ya gamu da wani almajirinsa. Ya tambayi almajirin: Ina za ka, wane? Sai ya ce: Ina guje wa jana’izar wan nan munafukin ne; kada in yi masa sallah. Sai Hussaini ya ce masa: Zo mu je ka tsaya a damana, duk abinda ka ji na fadi ka fada. Lokacin da liman ya yi kabbara a kan (mamacin) sai Hussaini ya ce: Allahu Akbar! Ya Allah, ka la’anci wane bawanka la’ana dubu, hadaddiya ba rababbiya ba. Ya Allah, ka wulakanta bawan nan naka a cikin bayi, ka shigar da shi zafin wutarka, ka dandana masa tsananin azabarka, domin ya kasance yana jibintar makiyanka, yana gaba da masoyanka, yana qin iyalin gidan Annabinka.”[15]

Jibintar makiyan Allah, a wajen ‘yan Shi’a, shi ne soyayya ga Sahabbai, gaba da masoyan Allah kuma kin Ahalul Baiti. Wadan nan su ne sifofin Ahalus Sunna da malaman Shi’a suke laka musu bisa qarya da zalunci. Ahalus Sunna suna son, kuma suna jibintar, Sahabbai da Ahalul Baiti dukkaninsu, Allah ya kara yarda a gare baki daya.

Har yau, Alhurrul Amili ya ruwaito a cikin littafinsa, Wasa’ilus Shi’a, daga Abu Abdillahi wai y ace, “Idan (mamacin) mai musun gaskiya ne sai ka ce: Ya Allah, ka cika cikinsa da wuta, ka cika kabarinsa da wuta, ka aiko masa da macizai da kunami!”[16]

Ya dan uwa mai karatu, dubi wannan kiyayya da keta da mugun nufi dake cike da zukatan ‘yan Shi’a, kuma suna dangana shi bisa karya ga zababbun bayin Allah, shiyagabannin Ahalul Baitti. Muna rokon Allah ya shirye su, ya shiryatar da mu baki daya.

Shin Gaskiya Ne ‘Yan Shi’a Suna Son Ahalul Baiti?

Babban makamin Takiyya da ‘yan Shi’a suke amfani da shi, shi ne son iyalin gidan Annabi(SAW), watau Ahalul Baiti, da jibintar su, da goyon bayan su. Amma wannan da’awa tasu, maganganunsu da rubuce-rubucensu suna karyata ta. Za mu kawo misalai na irin wadan nan maganganu nasu wadanda muka tsamo daga cikin littafan manyan malamansu.

Tabargazarsu Ga Annabi(SAW)

Da farko dai ‘yan Shi’a sun yi wa Annabi(SAW) cin fuska ta hanyar zargin iyalinsa, watau Innar Muminai A’isha(RA), da zina, da nacewarsu a kan wannan zargi duk da kubutarwa, da barrantarwa, da wankewa da Alkur’ani ya yi mata daga wannan zargin. Sa’an nan, suka zargi manyan Sahabbansa, kuma surukansa, da liwadi, watau Umar binul Khaddabi uban matarsa Hafsa da Usmanu binu Affan mijin diyansa biyu, Rukayya da Ummu Kulthum. Babu shakka a cikin wannan zargi ga wadanda suke kusa da Annabi, yake son su, kuma ya yarda da su, akwai cin fuska ga Manzo(SAW) da keta irili da suka mummuna.

Amma ‘yan Shi’a ba su tsaya a nan ba. A’a sun fito fili sun fadi wasu munanan maganganu da suke nuna suka ga Annabi(SAW) kai tsaye. Ba za mu kawo misalai masu yawa ba saboda muninsu, amma za mu ba da misali daya rak saboda mai karatu ya gani da idanunsa irin abinda ‘yan Shi’a suke fadi a hakkin Annabinmu Muhammad(SAW), kuma ya san cewa da’awar son Ahalul Baiti Takiyya ce kawai suke yi. Ibnu Taimiya ya hakaito fadinsu cewa, “A ranar lahira za’a kona al’aurar Annabi (SAW), saboda ya auri A’isha.”[17] Wal iyazu billahi!!

Wannan danyar magana, wacce take nuna kafircin mai faxin ta, ‘yan Shi’a na wannan zamani suna maimaita ta, kamar yadda ya zo a littafin Kashful Asrari wa Tabri’atil A’immatil Adhari na Sayyid Hussain Almusawi. Ya rubuta cewa, xaya daga manyan malaman Shi’a na wannan zamani, mai suna Sayyid Ali Garawi, ya ce: “Lallai Annabi (SAW) babu makawa sai al’aurarsa ta shiga wuta saboda ya auri wasu mata mushirikai.”[18] Yana nufin Aisha da Hafsa, Allah ya qara musu yarda.

          Wannan magana ba ta bukatar wani dogon sharhi. Babu shakka cewa, wanda duk yake kudure cewa SILIN GASHI DAYAna Annabi(SAW) zai shiga wuta, to wannan KAFIRI ne.

          Banda wannan, manyan malaman Shi’a suna zargin Annabi(SAW) da cewa ya gaza isar da aike. Ayatullahi Khumaini yana fadi a cikin littafinsa Kashful Asrari kamar haka, “A bayyane take cewa da Annabi ya isar da sako dangane da lamarin Imama gwargwadon yadda Allah ya umarce shi, kuma ya yi kokarin da ya kamata dangane da lamarin, da dukkan wannan sabani bai taso ba a kasashen Musulmi, kuma da ba’a samu kiyayya da yakoka ba, kuma da ba’a samu sabani ba a tushen addini da ressansa.”[19]

Sai mai hankali ya dubi wannan magana da abinda ta kunsa: Khumaini yana nufin Annabi(SAW) bai isar da aike ba kamar yadda Allah ya umarce shi, kuma shi ne sanadin gaba da qiyayya da yakoka tsakanin al’umma. Watau ke nan Annabi(SAW) BA RAHAMA BA NE SHI GATALIKAI, kamar yadda Allah ya sifanta shi a cikn Alkur’ani, tunda ya zama sanadin yakoka da kiyayya da gaba a tsakanin al’umma. Wal iyazu billahi!!

Har yau, wani malamin Shi’a na wannan zamanin, mai suna Jabir Agani, yana fadi dangane da Annabinmu(SAW) kamar haka: “Amincin Allah ya tabbata a gare ka, ya Ma’aikin Allah, amma ka yi kuskure, kuskure mai girma(!!) a yayin da ka fita daga duniya ba tare da ka yi wasiya ga kowa ba (dangane da al’amarin Imama). Kai za ka dauki alhakin hayaniyar da al’umma ta afka a ciki, da fitintinun da take fama da su. Don me ba ka yi wasiya ba, ya Ma’aikin Allah?!”[20]

Sai mu duba wannan magana da kyau, ya ‘yan uwa Musulmi. Akwai kafircin da ya wuce mutum ya ce: ANNABI(SAW) YA YI KUSKURE,KUMA BAI ISAR DA AIKEN ALLAH BA? Wal iyazu billah!!

Wannan ita ce maganar masu da’awar cewa suna son iyalin gidan Annabi(SAW), watau Ahalul Baiti, kuma suna jibintar su, suna goyon bayan su!! A bayyane take cewa wannan da’awa Takiyya ce kawai.

Tabargazarsu Ga Ali(RA)                        

A cikin kokarinsu na bata sunan shugabannin Musulunci da siffanta su da siffar marasa mutunci, malaman Shi’a suna dangana maganganu masu yawa ga Sarkin Musulmi Ali binu Abi Dalib, Allah ya kara masa yarda, irin maganganun da ba mai furta su sai wanda ya kai matuka a rashin mutunci. Babban malaminsu mai suna Muhammad Bakir Almajalisi ya ruwaito cewa: Wata mace ta mike a cikin masallaci, alhalin Sayyidina Ali yana yin huduba, sai ta ce, “Ya kai makashin masoya!” Wai sai Sayyidina Ali ya dube ta, ya ce: “Ya ke mara kunya, ya ballagaza. Ya wacce ba ta haila kamar yadda mata ke haila. Ya wacce a kan abin naninta akwai wani abu da ya burtso, yana reto.”[21] “ABINNANI,” wannan fassarata ce, amma shi mai ruwayar ya yi amfani da wata kalmar Larabci da take nufin FARJI, wacce idan da za mu fassara ta zuwa Hausa to da sai dai mu koma ga tsohuwar Hausa ta Maguzawa mu nemo kalmar.

Saboda Allah, ya xan uwa mai karatu, tana yiwuwa Ali binu Abi Dalib, Allah ya kara masa yarda, ya furta wadannan kalmomi, alhali yana kan mimbari yana huduba a masallaci? Kuma idan ya yi nufin ladabtar da wannan matar ne, ko mayar mata da martani, babu wasu kalmomin da suka fi dacewa da matsayinsa na Sahabi, kuma kanin Annabi(SAW), wanda ya taso aka raine shi a gidan Annabta? Babu shakka wannan kokarin bata sunan Ali ne, da ma sauran Ahalul Baiti, da ‘yan Shi’a suke yi, kuma a lokaci guda suna fakewa (suna yin Takiyya) da cewa wai su masu kaunar su ne.

Har yau, akwai wani labari da ‘yan Shi’a suke bayarwa cewa, wai wata rana wata mace ta yi wa wani mutum kazafi, sai ta dauki ruwan kwai farin, ta zuba shi a tsakanin kafafunta, ta ce wai ya yi lalata da ita, kuma wannan maniyyinsa ne. Wai sai Ali binu Abi Dalib(RA) ya tashi, ya duba tsakanin kafafunta, ya ce karya take yi, wannan ba maniyyi ba ne!![22]

Mai karatu, sai ka duba wannan magana da idanun basira. Ta qaqa Ali zai duba tsakanin kafafun mace muharrama don kawai ya tabbatar da karya ko gaskiyarta?! Shin duka garin ba wata mace wacce za’a sa ta yi wannan aikin? Shin wannan ba kokarin zubar da mutuncin Sarkin Musulmi Ali ba ne?

 

Tabargazarsu Ga Nana Fadima(RA)

Malaman Shi’a sun siffanta Nana Faxima, Allah ya kara mata yarda, da siffofi wadanda suke nuna matukar suka da zubar da girma. A nan ma, za mu takaita saboda munin wadannan siffofin.       A dangane da gadonta da suka ce wai Khalifa Abubakar Siddik ya hana ta, kuma wai Umar ya daure masa gindi a kan haka, suna ruwaito yadda ita Fadima din ta kai gwauro ta kai mari don neman gadon nata. Suka ce, “Fadima(AS) ta iske Abubakar da Umar a masallaci, ta yi musu maganar gadonta na gonar Fadak, inda ta yi fada da su, ta yi kururuwa, mutane suka taru, kuma ta kama wuyan Umar ta jawo shi zuwa gare ta.”[23]

Mai karatu ya dubi yadda wannan ruwaya ta siffanta Fadima: matar aure, Musulma, ta iske mazaje, abokan ubanta (kuma surukansa), a bainar jama’a, ta yi fada da su a kan gona, har ta ci kwalar dayansu!! Shin idan ma wannan gadon ya dame ta, ba ta da miji, ko wani dan uwa, da zai karbo mata hakkinta? Ai ba Fadima ba, wacce take Balarabiya, Bakuraishiya, Bahashima, kuma ‘yar Manzon Allah(SAW), ko wata ‘yar Fulani Bakanuwa, ba za ta aikata wannan rashin mutuncin ba. Amma abin mamaki shi ne, ‘yan Shi’a sun yarda da wannan ruwaya, kuma suna kattaba ta a cikin littafansu!!

Irin wadan nan maganganu na batanci da ‘yan Shi’a suke dangana wa Ahalul Baiti suna da yawa ainun a cikin littafansu. A nan, mun kawo dan misali ne kawai don mu tabbatar wa da mai karatu cewa da’awar kaunar iyalin gidan Manzon Allah(SAW) da Shi’awa suke yi munafurci ne kawai da yaudara da Taqiyya!!

Muhimmiyar Sanarwa

        Dukkanlittafan malaman Shi’a, da muka yi amfani da su a rubutun wannan takaitaccen littafi, akwai su a dakin karatu (laburare) na cibiyar Markazus Sahabah dake Sakkwato. Laburaren a bude take ga kowa da kowa.

 

Tare da gaisuwar dan uwanku a Musulunci

Dr. Umar Labdo

 

Pro 44

08026596528, 08095430077

 

[1] Duba Kashful Asrai na Ayatullahi Khumaini, bugun Teheran, 1363, shafi na 147.

[2] Duba littafinsa, Arrasa’il, bugun Qum-Iran, mujalladi na 2, shafi na 175.

[3] Arrasa’il, mujalladi na 2, shafi na 174.

[4] Duba Usulul Kafi na Muhammad binu Ya’akub Alkulaini, bugun Darul Murtadi, Bairut, Lebanon, 1426, mujalladi na 2, shafi na 219.

[5] A duba Taharirul Wasila na Khumaini, mujalladi na 1, shafi na 186.

[6] Duba littafinmu Matsayin Musulmi a Wajen ‘Yan Shi’a.

[7] A duba Ajwibatul Istifta’at na Ali Khamna’i, bugun Darul Hakki, Bairut, shafi na 178.

[8] Duba Masa’ilun Wa Rudud na Khu’i, bugun Kum, mujalladi na 1, shafi na 26.

[9] Duba littafinsa, Irshadus Sa’il, bugun Maktabatul Fakih, Kuwait, shafi na 39.

[10] Duba Majma’ul Masa’il na Kalbayakani, bugun Maktabatul Irfan, Kuwait, mujalladi na 1, shafi na 194.

[11] A duba littafin Arrasa’il na Khumaini, bugun Qum, 1385 B.H., mujalladi na 2, shafi na 196.

[12] Duba littafinmu, Bacin Tafarkin ‘Yan Shi’a, babin Fikihun ‘Yan Shi’a.

[13] ‘Yan Shi’a suna danka wasika a hannun mamatansu, su bunne su da ita. Wani kaset da suka nuna yadda suke jana’iza a nan Nijeriya ya tabbatar da haka. Nemi kaset din don ka gane wa idanunka.

[14] Duba littafin Almuqni’ah na Binu Nu’uman Almufid, bugun Mu’asasatun Nashril Islami, Qum-Iran, shafi na 85.

[15] Wannan ruwaya Aldusi ya fitar da ita a cikin littafinsa, Tahzibul Ahakami, mujalladi na 3, shafi na 197; da Ibnu Babawaihi Alqummi a cikin Man La Yahaduruhul Fakih, mujalladi na 1, shafi na 105; da Alhurrul Amili a cikin Wasa’ilus Shi’a, mujalladi na 2, shafi na 771.

[16] Duba Wasa’ilus Shi’a na Muhammad binul Hassan Alhurrul Amili, mujalladi na 2, shafi na 771.

[17] Duba Majmu’ul Fatawa na Ibnu Taimiya, bugun Saudi Arabiya, mujalladi na 28, shafi na 262.

[18] Duba Kashful Asrari na Musawi, bugun Darul Iman, Iskandariyya, 2002, shafi na 21-22.

[19] Duba Kashful Asrari na Khumaini, shafi na 50.

[20] A duba Shafin Gizo mai adireshi kamar haka: http://www.youtube.com/watch?v=l 8s KGuwa 4o.

[21] Duba Biharul Anwari na Muhammad Baqir Almajalisi, bugun Ihiya’ut Turathi, Bairut, 1403, mujalladi na 41, shafi na 293.

[22] Duba Biharul Anwari na Majalisi, mujalladi na 4, shafi na 303.

[23] Duba Kitab Salim binu Qais na Salim binu Qais Alhilali, bugun Mu’assasatul Bi’itha, Bairut, ba tarihi, shafi na 253.

 

 

Leave a comment