MUTU`AR `YAN SHI`A

Jerin Littafan Shi’a Na 4

Auren Mutu’a

a wajen

‘Yan Shi’a

Dr. Umar Labdo

 

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم

Ma’anar Mutu’a: Auren Wucin Gadi

Mutu’a, ko kuma auren wucin gadi, watau auren da ba na dun-dun-dun ba, ma’anarsa shi ne namiji ya kulla jinga da mace cewa zai sadu da ita sau daya ko sau biyu, ko kuma na tsawon awa daya, ko kwana kaza, ko wata kaza, a kan kudi kaza ko ladan abu kaza.

Auren Mutu’a yana cikin aurace-auracen Jahiliya kuma an yi aiki da shi a farkon Musulunci kana daga bisani aka haramta shi. An karbo ruwaya daga Ali binu Abi Dalib (R.A), cewa “Manzon Allah (SAW) ya hana auren Mutu’a da cin naman jakin gida a lokacin (yaqin) Khaibar.”[1]

Amma ‘yan Shi’a sun ci gaba da halasta Mutu’a kuma sun qago ruwayoyin qarya wadanda suka nuna falalarta da dumbin ladan wanda ya yi ta, da kuma darajarsa a aljanna. Babu shakka sun yi haka domin su bata al’ummar Musulmi ta hanyar yada lalata da barna da alfasha a tsakaninsu kuma don su jawo hankalin jahilai, musamman matasa, zuwa ga tafarkinsu.

Falalar Mutu’a

Akwai daruruwan ruwayoyi a cikin littafan malaman Shi’a da suke izna da su wadanda suke nuna falalar auren wucin gadi. Ya zo a cikin littafin Man La Yahduruhul Fakih, daya daga cikin littafansu guda hudu mafiya inganci, sun laka ma Ja’afar Sadik, Imaminsu na shida, cewa ya ce: “Lallai Mutu’a addinina ce kuma addinin iyayena. Wanda ya yi aiki da ita ya yi aiki da addininmu kuma wanda ya yi inkarin ta ya yi inkarin addininmu, kuma ya yi riko da wanin addininmu.”[2]

Ya zo a wannan littafi har yau, sun dangana ga Annabi (SAW) cewa wai ya ce: “Wanda ya yi Mutu’a sau daya zai amince fushin Allah, wanda ya yi Mutu’a sau biyu za’a tashe shi tare da zababbun bayi, wanda ya yi Mutu’a sau uku zai hada kafada da ni a aljanna.”[3] A wata ruwayar mai kama da wannan, sun kaga wa Manzon Allah (SAW) cewa wai ya ce: “Wanda ya yi Mutu’a sau daya za ta zama (gare shi) kamar darajar Hussaini (A.S); wanda ya yi Mutu’a sau biyu darajarsa kamar darajar Hassan (A.S) ce; wanda ya yi Mutu’a sau uku darajarsa za ta kasance kamar darajar Ali (A.S); kuma wanda ya yi Mutu’a sau hudu darajarsa kamar darajata ce.”[4]

Da yake mata suna da karin kunya a kan maza, wataqila za su bukaci a kara dan ingiza su kadan kafin su fada ramin alfasha. Don haka Alkummi, wanda suke yi wa lakabi da Alsaduk (watau mai yawan gaskiya!) ya kitsa musu tasu ruwaya ta musamman. Ya ce, “Lokacin da aka yi isra’i da Annabi (SAW) zuwa sama, ya ce: Jibrilu ya riske ni ya ce: Ya Muhammad, Allah mai girma da daukaka yana cewa: Lallai ni na gafartawa masu yin Mutu’a daga matayen al’ummarka.”[5]

Ladan Mai Yin Mutu’a

Abinda ya gabata dangane da falala da daukakar darajar mai yin auren Mutu’a ne. Amma dangane da dumbin ladan da zai samu, bari mu saurari Alsaduq ya kara shara mana ita. Ya ce: an tambayi Abu Abdullahi, watau Imamin Shi’a na shida: Shin mai yin Mutu’a yana da lada? Sai ya ce, “In yana nufin yardar Allah da ita (Mutu’ar) ba zai yi magana da ita ba (matar) kalma guda face Allah ya rubuta masa lada da ita (kalmar), kuma idan ya kusance ta sai Allah ya gafartar masa zunubi, kuma idan ya yi wanka Allah zai gafarta masa da gwargwadon ruwan da ya shude a kan gashinsa.”[6]

Gargadi ga Wanda Ya Qi Yin Mutu’a

Bayan bayanin falala da garabasar Mutu’a, idan da akwai wani mai taurin kai wanda ya ki dibar wannan garabasa, to sai a yi masa gargadi kuma a tsoratar da shi.   Wannan shi ne abinda malamin Shi’a, mai suna Alfailul Kashani, ya yi a yayin da ya ruwaito daga Annabi (SAW) cewa wai ya ce: “Wanda ya fita daga duniya bai yi Mutu’a ba, zai zo ranar Alkiyama yana yankakke (watau nakisin halitta).”[7] A harshen Shari’a, irin wannan gargadi ana yin sa ne ga wanda ya aikata kaba’ira, watau babban zunubi, kamar shaidar zur, ko gudu daga fagen fama, ko saba wa iyaye da sauransu. Saboda haka za mu fahimta a nan cewa, kin yin Mutu’a dai-dai yake da aikata kaba’ira. Kuma wannan babu mamaki idan muka dubi waccan ruwaya da ta gabata wacce take cewa, “Wanda ya yi inkarinta ya yi inkarin addininmu.”

Wannan ya sa Sayyid Hussain Almusawi, wanda a da dan Shi’a ne kuma Allah ya shirye shi ya tuba, yake cewa manyan malaman Shi’a na wannan zamani, kamar su Sayyid Assadar da Alburujardi da Asshirazi da Alkazwini da Aldibadiba’i da Abu Harith Alyasiri da kuma uban tafiya, Imam Khumaini, duka suna yin Mutu’a, kuma suna yin ta da yawa ba kadan ba![8]

A bisa mafi rinjayen zato, Rafilawan Nijeriya ma suna yin mutu’a, kuma Mutu’a na cikin hanyoyin yaudara da suke jawo hankalin jahilai da su, musamman matasa maza da mata, zuwa ga wannan tafarki nasu mai nufin rushe durakun al’umma.

Daurin Auren Mutu’a

Domin mai karatu ya gamsu da cewa Mutu’a qofar zina ce kawai aka budewa mutane, bari mu duba yadda ake yin daurin aure a tsarin Mutu’a. Auren Mutu’a ba ya bukatar a samu wakilin “ango” ko waliyin “amarya”, ba ya bukatar shaidu; ba’a ma bukatar kowa ya sani, kuma bai bukatar wani bata lokaci. Da zarar an hadu sai kawai a yi a gama!

Malaman Shi’a sun ruwaito cewa wani almajirin Imam Ja’afar Sadiq ya tambaye shi: “Ya zan ce da ita idan na kadaita da ita? Sai ya ce: Ka ce: Ina auren ki auren Mutu’a a bisa Littafin Allah da Sunnar Annabinsa; ba kya gado, ba’a gadon ki; kwana kaza kaza, ko shekara kaza kaza, a kan dirhami kaza kaza, sai ka ambata mata ladan da kuka yi yarjejeniya a kai, kadan ne ko da yawa.”[9]

Ina son mai karatu ya lura da yadda mai tambayar ya yi tambayarsa: “Ya zan ce da ita idan na kadaita da ita?” A ina a duniya aka san aure a cikin kadaitaka, a kebe? Babu wani addini a duniya, ko wata al’ada, inda ake aure a kebe. Babu inda ake aure a sirri sai a addinin Shi’a.

Wannan kawai ya isa ya tabbatar wa da mai karatu nisan wannan launi na aure da addinin Musulunci. A Musulunci, ana so a daidaita labarin aure, a kururuta shi, a yada shi, a kwaza shi, a yi talla da shi har duniya ta sani. Hadisai masu yawa sun zo da haka. Albani ma kadai, a cikin littafinsa Adabuz Zifafi, hadisai shida ya kawo, duka suna nuna wannan ma’ana. Ga biyu daga cikinsu don misali:

1. “Ku yi shela da aure.”[10]

2. “Bambancin tsakanin halal da haram (a aure) buga ganga.”[11]

Dubi yadda Manzo(SAW) ya kwaxaitar a buga ganga, duk da kyamar da Musulunci yake ga kida, don a kwarmata aure!

Sadaki ko Lada?

Abin sha’awa ne yadda malaman Shi’a ba sa kiran sadakin auren Mutu’a da sunan sadaki, sai dai su ce ujura, watau lada. Duk littafan da na duba ba inda suka kira shi da sunan sadaki. Wataqila a cikin wannan akwai matashiya, amma fa ga masu hankali!

Bari mu kira shi yadda suka kira abinsu: Mene ne ladan auren Mutu’a? Suka ce an tambayi Abu Ja’afar, Imamin Shi’a na biyar, ya ce, “Dirhami zuwa sama.”[12] Dansa kuwa, Ja’afar Sadiq, ya ce, “Tafi daya na gari ko tafi daya na dabino.”[13]

Watau da Hausa muna iya cewa sadakin auren Mutu’a shi ne kwandala ko gwan-gwan daya na garin kwaki! Akwai wani addini a duniya da ya wulakanta mata kamar addinin Shi’a? Allah ya tsare matan Musulmi da irin wannan kaskanci!

Da Wa Ake Mutu’a?

Shin sai da Musulma kawai ake Mutu’a? A’a sam! A cikin daren ‘yan Shi’a, ko kyankyaso ma nama ne! Don haka suka rawaito daga Imaminsu na shida, Ja’afar Sadik, (Allah ya isar masa karerayin da aka laka masa), wai ya ce, “Babu laifi mutum ya yi Mutu’a da Bamajusiya.”[14] Kuma ana yi da Banasariya (Kirista) da Bayahudiya, kamar yadda suka ruwaito daga Imaminsu na takwas, Abul Hassan Ali binu Musa Rida,[15] Haka nan ana yi da karuwa domin, kamar yadda suka ce, sai ya hana ta karuwanci![16]

Ana Yi da Matar Aure!

Dangane da yin Mutu’a da matar aure (watau matar wani) akwai ruwayoyi guda biyu masu ban mamaki wadanda ya kamata mai karatu ya gan su da idanunsa. Ta farko an karbo ta daga Falalu Maulan Muhammad binu Rashid, ya ce da Ja’afar Sadiq: “Ni na auri wata mace auren Mutu’a sai ya darsu a raina cewa tana da miji. Da na bincika sai na samu ashe tana da miji. Sai Ja’afar ya ce: Don me ka bincika?!”[17] A wata ruwayar, sai ya ce, “Wannan (binciken) ba ya kanka. Abinda yake kanka kawai shi ne ka gaskata ta dangane da kanta.” [18]

Ruwaya ta biyu ita ma Kulaini da kansa (watau Bukharin ‘yan Shi’a) shi ne ya ruwaito ta. An karbo daga Abanu binu Taglub ya ce: “Na ce da Abu Abdullahi (watau Ja’afar Sadik) ni ina tafiya a kan hanya sai in ga mace kyakkyawa kuma ba ni da tabbas ko tana da miji ko karuwa ce. Sai ya ce: Wannan (binciken) ba ya kanka. Abinda yake kanka kawai shi ne ka gaskata ta dangane da kanta.”[19] (Watau idan ta ce ba ta da miji shi ke nan.)

Wannan yana nufin cewa shi dan Shi’a babu abinda ya dame shi! Idan al’amari ya motsa masa, to ko matar wa yana kamawa.   Shin muna iya cewa wadanda suke zaune tare da Rafilawa suna cikin hatsari? Amma ba wannan ne kawai hatsarin ba; ga wanda ya fi shi.

Ana Yi da Karamar Yarinya!

Ana yin Mutu’a da karamar yarinya wacce ta kai shekara goma. An tambayi Abu Abdullahi, “Ko mutum na iya yin Mutu’a da yarinya karama? Sai ya ce: E, sai dai idan karama ce ainun ta yadda ana iya yaudararta. Aka ce: Nawa ne idan ta kai ba’a yaudarar ta? Ya ce: Shekara goma.”[20]

Imam Khumaini, shugaban ‘yan Shi’ar duniya na wannan zamani, ya yi wani dan ijitihadi a nan. Ya ce karamar yarinya da jaririya duka ana iya yin Mutu’a da su amma ba da hakikanin saduwa ba, sai dai da sumbata da runguma da kuma abinda ya kira ‘cinyantaka’ [tafkhiz], watau mutum ya sa zakarinsa a tsakanin cinyoyinta. Sai mai karatu ya gafarce mu saboda ruwaito wannan danyar magana, maras dadin ji, amma haka Imamin ya fadi, kuma maganar tana cikin littafinsa da ya rubuta da hannunsa.[21]

Wannan ijtihadi na Imam Khumaini ba a ilmance kawai ya tsaya ba; a’a ya aiwatar da shi a aikace. Sayyid Hussaini Almusawi ya ba da labarin Mutu’a da Khumaini ya yi da wata yarinya mai shekara hudu ko biyar a duniya, a lokacin da yake zaman gudun hijira a kasar Iraki kafin juyin juya halin da ya shugabanta a Iran, a shekara ta 1979. Mai son ganin wannan labari filla –filla, sai ya duba Kashful Asrari na Almusawi, shafi na 35-37.

Ba wani abu ya sa muka bi diddigin wannan mas’ala ba sai don mai karatu ya san cewa mutanen da gaske suke. Allah ya yi mana Alam Nasharaha!

Mai Mutu’a, Matanka Nawa?

Amsa ta gaskiya, tsakani da Allah, ita ce: Ba iyaka! ‘Yan Shi’a sun ruwaito daga Imaminsu na biyar, Abu Ja’afar, ya ce: “Mutu’a ba da mata hudu ba ne kawai; domin ita (mace mai Mutu’a) ba’a sakin ta kuma ba ta gado, ba’a gadon ta. Ita mai jinga ce kawai.”[22]

Har yau, sun ruwaito daga Imaminsu na shida, Abu Abdillahi, cewa an tambaye shi dangane da Mutu’a: Ana iyakance ta da mata hudu? Sai ya ce, “Ka auri dubu; su ‘yan jinga ne kawai.”[23]

Lutsu Da Mata

        Malaman Shi’a kazamai suna halasta yin luwadi da mata kuma suna dangana halaccin wannan ta’asa ga Imamansu a bisa karya. Sun dangana haka ga Imaminsu na shida, Abu Abdillahi Ja’afar Sadik. Suka ce wani almajirinsa mai suna Abul Ya’afur ya ce, “Na tambayi Abu Abdillahi(AS) dangane da halaccin mutum ya zakkewa mace ta duburarta. Sai ya ce: Babu laifi idan ta yarda.”[24] Haka nan sun dangana halaccin wannan kazanta ga Imaminsu na takwas, Abul Hassan Musa Rida.[25]

Uban tafiya, Ayatullahi Ruhullahi Khumaini, yana daga cikin malaman Shi’a masu ganin halaccin al’amarin. Ga abinda ya ce: “Ra’ayi mafi karfi, kuma mafi bayyana, shi ne halaccin saduwa da mace ta duburarta.” Haka nan ya fadi ba sayawa, ba sakayawa.[26]

Babu shakka wannan ra’ayi na ‘yan Shi’a ya sabawa Alkur’ani mai girma inda Allah Madaukaki yake cewa, “To idan sun yi wanka (watau matayenku) sai ku je musu daga inda Allah ya umarce ku.” (Suratul Baqara: 222). Malaman Tafsiri sun hadu a kan cewa abin nufi da ‘inda Allah ya umarce ku’ shi ne farji, ba dubura ba. Haka nan kuma ya saba da hanin Annabi(SAW) inda yake cewa, “Kada ku zakkewa mataye ta duburarsu.”[27]

Muna rokon Allah Madaukaki ya tsarkake mazan al’ummar Annabi da matanta daga wannan kazanta ta Majusawa.

Aron Farji

        Manyan malaman Shi’a suna halasta aron farji. Sayyid Hussain Musawi ya yi bayanin ma’anar aron farji kamar haka: “Aron farji ma’anarsa shi ne mutum ya bayar da matarsa ko baiwarsa ga wani mutum dabam sai ya halasta gare shi ya ji dadi da ita ko kuma ya yi duk abinda ya ga dama da ita. Idan mutum ya yi nufin tafiya sai ya bar matarsa a wajen maqwafcinsa, ko abokinsa, ko kuma duk mutumin da ya zaba, sai ya halasta a gare shi ya yi abinda ya ga dama da ita a tsawon tafiyar mijinta.”[28]

Don halasta wannan barna, malaman Shi’a suna dangana ruwayoyi ga Imamansu a bisa qarya. Daga cikin irin wadan nan ruwayoyi, akwai abinda suka dangana ga Abu Abdullahi. Aldusi ya karbo daga Abul Hassan Addari’i, ya ce: “Na tambayi Abu Abdillahi (A.S) dangane da aron farji, sai ya ce: Babu laifi.”[29] Har yau, Aldusi ya karbo daga Zuraratu, ya ce: “Na tambayi Abu Ja’afar (A.S) dangane da mutum ya halasta wa dan uwansa farjin baiwarsa. Sai ya ce: Babu laifi; abinda ya halasta masa daga gare ta ya halasta gare shi.”[30] Babban malamin Hadisi a wurin ‘yan Shi’a, wanda suke daukar sa kamar yadda Ahalus Sunna suka dauki Imam Bukhari, watau Muhammad binu Ya’aqub Alkulaini, shi ma ba’a bar shi a baya ba. Ya ruwaito cewa, Imaminsu na shida Abu Abdillahi Ja’afar Sadik, ya ara wa almajirinsa, Muhammad binu Mudarib, wata kuyanga a lokacin da ya ziyarce shi. Ga abinda almajirin yake cewa: “Abu Abdullahi (A.S) ya ce mini: “Ya kai Muhammad, riki wanan baiwa ta yi maka hidima kuma ka shafe ta (ka sadu da ita). Idan za ka tafi, sai ka komo mana da ita.”[31]

Duba ka gani dan uwa mai karatu, Allah ya tsarshe ni tare da kai daga sharrin ‘yan Shi’a da batansu, yadda Rafilawa suka kai matuka wajen kokarin yada lalata da alfasha a tsakanin al’umma ta hanyar halasta zina da kira karya a dangana ta ga zababbun bayin Allah.

Mu imaninmu shi ne, wannan ruwaya da aka dangana wa Ja’afar Sadik karya ce aka yi masa. Imam Ja’afar Sadiq ba zai bar tafarkin kakansa Annabi(SAW) ba, ya bi tafarkin Majusawa.

Muhimmiyar Sanarwa

Dukkan littafan malaman Shi’a da muka yi amfani da su wajen rubuta wannan takaitaccen littafi ana samun su a laburaren cibiyar Markazus Sahabah dake Sakkwato Birnin Shehu, kuma mai son ya ga wadannan littafai yana iya yin haka ba tere da wata matsala ba. Laburaren buxe take ga kowa da kowa.

 

Muhimmiyar Sanarwa

        Dukkanlittafan malaman Shi’a, da muka yi amfani da su a rubutun wannan takaitaccen littafi, akwai su a xakin karatu (laburare) na cibiyar Markazus Sahabah dake Sakkwato. Laburaren a bude take ga kowa da kowa.

 

Tare da gaisuwar dan uwanku a Musulunci

Dr. Umar Labdo

 

 

[1] Bukhari da Muslim.

[2] Ibnu Babawaih Alkummi, Man La Yahduruhul Fakih, bugun Darut Ta’aruf, Bairut, 1401 B.H., mujalladi na 3 shafi na 336.

[3] A duba Man La Yahduruhul Fakih na Alkummi, muj. na 3 sha. 336.

[4] Fatahallah Kashani, Tafsiru Minhajis Sadikin, bugun Maktabatus Sadar, Tehran-Iran, 1379 B.H., muj. na 2 sha. na 493.

[5] A duba Man La Yahduruhul Fakih, muj. na 3 sha. na 463.

[6] Man La Yahduruhul Fakih, muj. na 3 sha. na 336.

[7] A duba Minhajus Sadikin na Kashani, muj. na 2 sha. na 489.

[8] Sayyid Hussain Musawi, Kashful Asrari wa Tabri’atil A’immatil Adhari, bugun Darul Iman, Alkahira, 2002, sha. na 34-35.

[9] Muhammad binu Ya’akub Alkulaini, Furu’ul Kafi, bugun Darul Murtali, Bairut, 1428 B.H., muj. na 5 sha. na 455.

[10] Albani ya ce Ibnu Hibban da Dabarani da Diya’u Almaqdisi duka sun ruwaito shi, kuma isnadinsa mai kyau ne. Duba Adabuz Zifafi na Albani, bugun Almaktabul Islami, 1409/1989 sha. na 111-112.

[11] Albani ya ce Nasa’i da Tirmizi da Ibnu Majah sun ruwaito shi da isnadi kyakkyawa. Duba Adabuz Zifafi, sha. na 111.

[12] A duba Furu’ul Kafi na Kulaini, muj. na 5 sha. na 457.

[13] Furu’ul Kafi, muj. na 5 sha. na 457.

[14] Abu Ja’afar Muhammad binul Hassan Aldusi, Tahzibul Ahkam, bugun Darul Adwa, Bairut, 1406 B.H., muj. na 7 sha. na 256.

[15]Tahzibul Ahkam, muj. 3 shafi na 144.

[16] Tahzibul Ahkam, muj. na 7 sha. na 253. Kuma a duba Tahrirul Wasila na Ayatullah Ruhullah Khumaini, bugun Darul Ilmi, Kum-Iran, ba tarihi, sha. na 295.

[17] Tahzibul Ahkam na Aldusi, muj. na 7 sha. na 253.

[18] Furu’ul Kafi na Kulaini, muj. na 5 sha. na 469.

[19] Furu’ul Kafi, muj. na 5 sha. na 462.

[20] A duba Furu’ul Kafi, muj. na 5 sha. na 463; da Tahzibul Ahkam na Aldusi, muj. na 7 sha. na 255.

[21] A duba Tahrirul Wasila na Khumaini, muj. na 2 sha. na 241.

[22] Abu Ja’afar Muhammad binul Hassan Aldusi, Al’istibsar Fi Ma Ikhtalafa Minal Akhbar, bugun Darul Kutubil Islamiyya, Tehran-Iran, 1390 B.H., muj. na 3 sha. na 147.

[23]A duba Al’istibsar na Aldusi, muj. na 3 shafi na 147; da Tahzibul Ahkam shi ma na Aldusi, muj. na 7 sha. na 259.

[24] A duba Al’istibsar na Aldusi, muj. na 3 sha. na 243.

[25] Al’istibsar, muj. na 3 sha. na 243.

[26] Duba littafinsa, Tahrirul Wasila, muj. na 2 sha. na 241.

[27] Tirmizi da Nasa’i da Ibnu Maja duka sun fitar da Hadisin.

[28] Sayyid Hussain Musawi, Kashful Asrar, sha. na 46-47.

[29] A duba Al’istibsar na Aldusi, muj. na 3 sha. na 141.

[30] Al’istibsar, muj. na 3 sha. na 136.

[31] A duba Furu’ul Kafi na Kulaini, muj. na 2 sha. na 200.

 

 

Leave a comment